Shugaban ya kwashe makwanni da yawa baya ƙasar abinda ya haddasa cece-kuce mai zafi da nuna damuwa kan rashin snain inda ya shiga.
Shugaban mai shekara 91 a duniya ya bayyana a talabijin bayan saukar jirginsa a Younde, an kuma hangi yadda yake gaisawa da manyan jami'an gwamnati yayin da matarsa Chantal Biya ke kusa da shi.
Bayan kammala gaisawar ne jerin gwanon motocin shugaban ƙasar suka ɗauke shi inda aka hangoshi yana ɗagawa magoya baya hannu
Murna ta kaure da kiɗe-kiɗe bayan da shugaban ya sauka a filin jirgin, inda nan take ya zarce fadar shugaban ƙasa kamar yaddda gidan talabijin na CR ya nuna dawowar shugaban.
An hangi yadda magoya bayansa suka sanya riga ɗauke da hoton Paul Biya suna murnar dawowars aƙasar..
A baya bayannan ƴan ƙasar sun ta nuna damuwa da tambayar halin da shugaban ke ciki da ma halin lafiyarsa bayan nemansa da aka yi sama ko ƙasa aka rasa tun bayan da aka ganshi a watan Satumba lokacin da ya je ƙasar China da ƙasashen Afirka.
Shugaban ya sauka a jirgi mai lamba CMR001, kuma ya taso daga birnin Geneva inda ya kwashe makwanni yana zaune kamar yadda jami’an gwamnatin ƙasar suka tabbatar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI