Shugaban hukumar UNESCO na farko dan Afirka ya rasu yana mai shekaru 103

Shugaban hukumar UNESCO na farko dan Afirka ya rasu yana mai shekaru 103

Amadou Muhtar Mbow wanda ya jagoranci hukumar ta UNESCO daga shekarar  1974 zuwa 1987 jigo ne kuma abin koyi a kasar sa ta Senegal da ma nahiyar Afirka, wadda ya jajirce wajen samar da gagarumar ci gaba a bangarorin ilimi da zaman lafiya, kuma ya rasu ne yana mai shekaru 103, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar Senegal APS a jiya.

Da jin labarin rasuwar Farfesa Amadou Muhtar Mbow shugaban kasar ta Senegal Bassirou Diomaye Faye ya gabatar da ta’ziyarsa a shafinsa na X, yayin da ya bayyana shi a matsayin  wani muhimmcin gimshiƙi a fagen ci gaban al’uma.

Shugaban ya kara da cewa  Darakta janar din jigo ne ga al’umar Senegal wanda cike gurbinsa wani babban kalubale ga al’umar kasar.

Sannan shima firaministan kasar Ousmane Sonko ya bayyana cewa Senegal ta yi gagarumar rashi ta fasihi kuma mutum mai karsashi a fagen tattali da kuma raya al’adu na gargajiya da aka san al’uma dasu, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ci gaban kasar da ma nahiyar Afirka baki dayanta.

Darakta janar ta hukumar ta Unesco Audrey Azoulay ta karrama Mbow bisa na mijin kokarinsa da kuma yadda yabar baya da kyau daga irin ci gaban da ya samar a shugabancin hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.

Mbow  shine ɗan Afirka na farko da ya jagoranci wata hukuma ta kasa da kasa, wanda ya kasance abin koyi kuma cikakken haziki mai son ci gaban al’uma, ya kuma bar tarihi mai zurfi a cibiyar ta UNESCO ta hanyar kare bukatar hadin kai da daidaito tsakanin al'ummomi da al'adu.

An haifi Amadou Muhtar Mbow ne shi a shekara ta 1921 yayin da ƙasarsa ke ƙarƙashin mulkin mallaka na Faransa, a yayin da a rayuwarsa ya shiga tsaka mai wuya a yaƙin da ya fafata na neman ‘yancin kai na Senegal.

Bayan ya kammala karatu a Faransa, Mbow ya koma kasarsa inda ya karantar da tarihi da ilimin sanin taswirar duniya da sararin samaniya .

Wadda daga baya ya zama ministan ilimi da kuma na al'adu a karkashin shugaban kasar Senegal na farko Leopold Sedar Senghor.

A cikin 2008, yana mai shekaru 87, ya jagoranci babban taron kasa na Senegal, wadda aka gudanar da zummar neman mafita da hanyoyin magance matsalolin siyasa da zamantakewa na ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)