
Kagame da Tshisekedi za su halarci taron ƙungiyar ƙasashen yankin gabashin Afrika a birnin Dar es Salam na Tanzania, inda jagoroin yankin su 8 da na kudancin Afrika 16 za su gana.
Ƙungiyar ƴan tawayen M23, wadda Rwanda ke mara wa baya ta karɓe iko da yankuna da dama a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo mai ɗimbin arzikin albarkatun ƙasa sakamakon hare-harenta da su ka ɗaiɗaita dubban mutane.
A makon da ya gabata ne ƙungiyar ta ƙwace birnin Goma mai matuƙar mahimmanci, kuma yanzu haka tana ƙoƙarin rankayawa lardin ƙudancin Kivu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI