An zabi Assoumani a matsayin shugaban kasa karo na uku a jere shekarar da tagabata, bayan zabe mai cike da cece-kuce, inda ‘yan adawa suka tuhume shi da magudin zabe. Ba zai iya sake tsayawa takara a shekarar 2029 ba, amma tuni ya fara shirye-shiryen maye gurbinsa, inda ya shaida wa magoya bayansa a ranar Alhamis cewa idan lokacin da zai bar mulki ya yi, fatan sa ne dansa ya maye gurbinsa a matsayin shugaban kasar.
Shugaba Azali Assoumani, na Comoros © Présidence des ComoresA watan Oktoban da ya gabata ne ya baiwa dansa El Fath nauyin gudanar da ayyukan gwamnati tare da ba shi iko a majalisar ministocin kasar.
“Azali ya mika wa dansa hakkin shugaban kasa da na kundin tsarin mulki,” in ji Larifou, lauya kuma dan siyasa da ke gudun hijira, wanda ya shaidawa RFI a lokacin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI