Shugaban ƙasar Ghana ya samu nasarar sulhunta rikicin masarautu

Shugaban ƙasar Ghana ya samu nasarar sulhunta rikicin masarautu

Shugaban cibiyar tabbatar da zaman lafiya na ƙasar ta Ghana Dr. George Amoh ya jaddada muhimmancin da ziyarar shugaban ƙasar ta Ghana John Drama Mahama ya kai a Bawku, wadda ya ce wata hanya ce ta maido da cikakken zaman lafiya a yankin da ya daɗe cikin tashin tashina.

Amoh ya yi wannan bayani ne a yayin da yake zantawa da manema labaru, yayin da ya ke fasalta rawar da ziyarar ta taka da jagoranci na gaskiya da adalci wanda ya yi amfani da damarsa ta shugabanci wajen warware taƙaddamar saruta da aka shafe shekaru da dama ana tafkawa a yankin na Bawku.

Daktan ya ce "Batun amana na da matukar muhimmanci wajen samar da zaman lafiya a tsakanin al’uma, kuma ina ganin hakan shi ne babban kalubale a rikicin na Bawku.

Ya yi nuni da cewa rashin yarda da juna da ke tsakanin bangarorin biyu shi ne ya dagula kokarin da ake daɗe ana yi na ganin an cimma matsaya mai dorewa a baya.

Ziyarar ta Shugaba Mahama, a cewar Dr Amoh, ta aike da sako mai karfi ga al'ummar Bawku da ma al'ummar kasar baki daya a ɓangaren riƙon amana da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)