Shugaban ƙasar Ghana ya naɗa wanda zai gaji kujerar gwamnan babban bankin ƙasar

Shugaban ƙasar Ghana ya naɗa wanda zai gaji kujerar gwamnan babban bankin ƙasar

Shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya zabi Hohnson Asiamah a matsayin wanda zai kasance gwamnan babban bankin ƙasar, a yayin da yake jiran tabbatarwa ta majalisar zartaswar ƙasar a cewar fadar shugaban.

Asiamah dai ya shafe sama da shekaru 23 yana aiki a Bankin ƙasar  wato Banko of Ghana, sannan daga shekarar daga shekarar 2016 zuwa 2021 ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan babban bankin ƙasar.

Fadar shugaban ƙasar ta ci gaba da cewa, ya taka rawar gani wajen samar da kyawawan manufofi akan darajar kuɗin Ghana a ciki da wajen ƙasar tare da samar da bunkasar tattalin arzikin ƙasar.

Naɗin nasa yazo ne adaidai lokacin da wa’adin Gwamnan babban bankin ƙasar mai ci yazo ƙarshe a yain da Asiamah zai ɗare kujerar domin ci gaba daga inda ya tsaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)