Janar Christian Tsiwewe Songesha ya bar mukaminsa na shugaban rundunar sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo bayan shafe shekaru biyu yana jagorancinta.
Tsohon kwamandan Rundunar Tsaron fadar shugaban ƙasa, an kara masa girma zuwa babban hafsan hafsoshi a watan Oktoban shekarar 2022 tare da manufar dakile ci gaban ƴan tawayen M23, da ke samun goyon bayan Rwanda.
To sai dai ƙungiyar ta ci gaba da samun nasara a kan sojojin gwamnati, in da ya zuwa yanzu, M23 ke iko da yankuna masu yawa a Arewacin Kivu, da suka hada da Masisi, Rutshuru, Walikale, Nyiragongo da Lubero, yankunan da adadinsu ya ninka sau biyu a shekarar 2012.
Amma dai, duk da cire shi daga jagorantar rundunar sojin ƙasar, an naɗa Janar Tsiwewe a matsayin mai bawa shugaba Félix Tshisekedi shawara kan harkokin soji.
Yanzu Laftanar Janar Banza Mwilambwe Jules shine sabon shugaban rundunar sojin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI