Sanarwar fadar gwamnatin Chadi ta ce tagawar dake da rakiyar babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christophe Musu sun isar da wasikan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ga takwaransa na Chadi Mahamat Deby.
sanarwar ta ce wasikar na ƙunshe da sakon Tinubu na jajanta wa tare da jaddada goyon bayansa ga shugaban kasar da kuma al'ummar Chadi dangane da mummunar harin ta’addanci da ya hallaka sojojin ƙasar da dama a sansaninsu da ke tsibirin Barkharam kwanakin baya.
Barazanar janye dakarun Chadi
Ziyarar na zuwa ne makonni bayan da shugaban ƙasar Chadi Mahamat Idris Deby ya yi barazanar janye dakarunsa daga cikin rundunar hadin kai dake yaki da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi, saboda zargin da yake musu na gaza magance matsalar ta'addancin da ake yaki da shi.
A wata hira da aka yi da Mahamat Deby lokacin da yake ƙari haske kan harin ramuwa da sojojin ƙasar suka kai maɓuyar Boko Haram a Tafkin Chadi, ya ce rundunar da aka kafa domin hadin kai tsakanin kasashen yankin bata da wani tasirin da aka kafa dominsa ba, inda ya jaddada barazar ficewar sojojin ƙasar domin mayar da hankali wajen kare al'ummar Chadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI