Shugaba Faye ya rushe majalisar dokokin Senegal tare da sanya ranar sake zaɓensu

Shugaba Faye ya rushe majalisar dokokin Senegal tare da sanya ranar sake zaɓensu

Faye wanda ya lashe zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Maris na wannan shekarar, tare da faraministansa Ousmane Sonko, sun yi wa ƴan ƙasar alkawarin kawo sauyi mai ma’ana.

To sai dai gwamnatin su na fuskantar koma baya wajen aiwatar da manufofinta, sakamon rashin rinjayen da su ke da shi a zauren majalisar.

A cewar kundin tsarin mulkin Senegal, Faye na da ikon rushe majalisar dokokin da ke da rinjayen ƴan adawa, tare da sanya ranar da za a gudanar da zaɓensu don samun rinjayen da suke buƙata, wanda hakan kuma zai basu damar aiwatar da kudurorinsu.

Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye da tsoho shugaban ƙasar Macky Sall. Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye da tsoho shugaban ƙasar Macky Sall. AFP - -

Gwamnatin Faye dai na zargin gwamnatin magabacinsa ta Macky Sall, da kunbiya-kunbiya game da yadda gwamnatinsa ta kashe ƙudi.

Ya ce nan bada jimawa ba za su wallafa rahoton binciken da suka gudanar game da yadda gwamnatin baya ta kashe ƙuɗaɗe, bayan da kotun ƙasar ta amince da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)