Shugaban na Senegal ya na mia cewa"yayin da yakin neman zaben 'yan majalisar dokoki ke gabatowa, ina gayyatar dukkan 'yan kasar Senegal, musamman ma 'yan siyasa na ko wane bangare, da su guji wuce gona da iri a cikin maganganunsu da ayyukansu."
Wasu daga cikin masu goyon bayan Shugaban kasar Senegal AP - Mosa'ab ElshamyShugaban na Senegal ya yi amfani da wannan dama tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo ta su goyon baya na ganin an cimma nasara a wannan zabe da sunan ceto kasar ta Senegal a karshe da kuma tabbatar da cewa "zaben zai kasance cikin 'yanci, dimokiradiyya da gaskiya".
Sugaban Senegal Basirou Diomaye Faye. REUTERS - Abdou Karim NdoyeA ranar 17 ga watan Nuwamba ne 'yan kasar Senegal za su zabi sabuwar majalisar dokoki, watanni takwas bayan zaben shugaban kasar da Diomaye Faye ya yi nasara a zaben shugaban kasa da aka yi a zagayen farko da kashi 54% na kuri'un da aka kada. Za a fara yakin neman zaben a yau Asabar da dare.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI