Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karbi bakuncin Firaministan Libiya Fayez Al-Sarraj.
Ganawar da aka yi a Fadar Wahdettin da ke Istanbul ta dauki tsawon kusan awanni 2. Daga baya kuma sai jami'an bangarorin biyu suka gana da juna.
Sanarwar da Sashen Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya ya fitar ta ce, a ganawar an tattauna alakar kasashen biyu da kuma al'amuran da ke afkuwa a yankunansu.
A yayin ganawar Shugaba Erdogan ya sake jaddada cewar Turkiyya za ta ci gaba da kasancewa tare da Libiya, kuma suna ta kokarin karfafa alakarsu da halastacciyar Gwamnatin Sulhun Kasa ta Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.
Ya kuma ce abu ne mai dadi yadda Majalisar Dinkin Duniya ta rubuta bayanan iyakance kan iyakokin Libiya a teku karkashin yarjejeniyar da ta kulla da Turkiyya, kuma za su ci gaba da bayar da goyon baya don ganin al'umar Libiya sun samu walwala da jin dadi.