Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karbi bakuncin Firaministan Libiya Fayyaz Al-Sarraj.
Shugabannin sun gana a sirrance na tsawon awanni 2 da mintuna 35 a fadar Shugaban Kasar Turkiyya ta Wahdettin da ke Istanbul.
Sanarwar da Sashen yada Labarai na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya ta fitar ta ce a ganawar ta shugaba Erdogan da Sarraj, an mayar da hankali kan halin da ake ciki a Libiya.
Sanarwar ta ce "Shugaba Erdogan da Shugaba Sarraj tare da tattauna kan batutuwan da za su samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga jama'ar Libiya. A yayin tattaunawar, Shugaba Erdogan ya sake jaddada cewar Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan halastacciyar gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita a Libiya. Babban abun da Turkiyya ta fi damuwa da shi, shi ne a samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, hadin kan siyasa da tsaron kasa a Libiya."
Shugaba Erdogan ya kuma sake jaddada cewar samun zaman lafiya a Libiya, zai amfani kasashe makota, kasashen Larabawa da ma nahiyar Turai, a saboda haka ake da bukatar kasashen duniya su nuna goyon baya na gaskiya.
A yayin tattaunawar an sake jaddada ci gaba da aiki da yarjeniyoyin da Turkiyya ta sanya hannu tsakanin ta da Libiya, an kuma sake yin nazari kan aiyukan bayar da kariya da Turkiyya ke yi ga hakkokin Libiya a Gabashin Bahar Rum.