Cikin watan Janairun 2020 ne shugaba Embalo mai shekaru 51 ya hau kujerar mulkin Guinea Bissau bayan samun kashi 54 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa wanda ya bashi damar doke abokin takararshi Domingos Simoes Pereira tare da maye gurbin Jose Mario Vaz.
Sanarwar ta shugaba Embalo ta zo da bazata, ganin cewa ya na da damar iya sake yin wa’adi 1 na mulkin ƙasar ta Guinea a wani yanayi da rikicin siyasar ƙasar ya ta’azzara a ɓangare guda fargabar juyin mulkin Soji ta baibaye mulkin kasar mai yawan jama’a miliyan 2.
Bayan taron majalisar ministocinsa a daren jiya Alhamis ne shugaba Embalo ya sanar da wannan mataki na ƙin tsayawa takara a zaɓen wanda ake saran gudanar da shi cikin watan Nuwamba ko Disambar shekarar nan.
A cewar shugaban na Guinea Bissau ya sauya ra’ayi daga shirin tsayawa takarar ne saboda mai ɗakinsa wadda ba ta sahale mishi sake neman wa’adin mulki na gaba ba.
Embalo wanda ya ce magajin shi ko shakka babu ba zai kasance Pereira da ya doke a zaɓen 2020 ba, haka zalika ba zai kasance guda cikin jagororin adawarsa biyu da suka kunshi Braima Camara ko Nuno Gomes Na Bian ba.
Har zuwa tashi daga taron na daren jiya dai shugaba Sisico Embalo bai bayyana wanda ya ke goyon baya a matsayin magajin shi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI