
Tina Salama, wadda ita ce mai magana da yawun Shugaba Felix Tshisekedi ta ce baya ga gwamnatin haɗaka da shugaban ke shirin kafawa, akwai sauye-sauye da yake shirin yi a tsarin shugabancin ƙasar sai dai ba ta yi ƙarin haske dangane da yadda sauye-sauyen za su kasance ba..
Akwai yiwuwar Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Felix Tshisekedi ya kafa gwamnatin haɗaka a daidai lokacin da yake ci gaba da fuskantar matsin lamba a cikin gida dangane da yadda yake tafiyar da rikicin ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda.
A ranar Asabar, Shugaba Tshisekedi ya shaida wa wani taron jam’iya mai mulki kan cewa kada rikicin cikin gida ya ɗauke musu hankali: “Dole ne mu haɗa kanmu domin tunkarar maƙiya.”
“Shugaban ƙasar ya sanar da cewa zai karkata wurin kafa gwamnatin haɗaka ta ƙasa tare da yin sauye-sauye a tsarin jagorancin sacred union,” kamar yadda ta shaida a shafinta na X.
Batun kafa gwamnatin haɗakar na zuwa ne bayan Amurka da wasu ƙasashe sun buƙaci a tsagaita wuta a rikicin da ake yi a ƙasar.
Ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda na ci gaba da samun nasara a bangarpri da dama a fafatawar sukeyi da sojojin ƙasar ta Congo.
Kungiyar a yanzu haka tana rike da yankuna masu yawa na gabashin DRC, yankin da ke fama da rikici.
Yunkurin ci gaban da take samu ya sa dubban mutane tserewa daga yankunan.
Mayakan sun kwace iko da babban birnin lardin Kivu ta Kudu da Bukavu a ranar Lahadin da ta gabata, makonni bayan da suka kwace Goma, babban birnin Kivu ta Arewa kuma babban birnin da ke gabashin kasar.
A baya dai kwamitin sulhun ya yi kira da a gaggauta tsagaita buɗe wuta ba tare da wani sharadi ba, amma a ranar Juma'a dukkan kasashen da suka hada da mambobin ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afirka uku sun nuna yatsa a kan Kigali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI