Shin su wane Lakurawa dake barazana ga tsaron arewacin Najeriya?

Shin su wane Lakurawa dake barazana ga tsaron arewacin Najeriya?

Lakurawa na ayyukansu a arewa maso yammacin Najeriya a cewar hukumomin Najeriya, kuma mazauna yankin sun tabbatar da cewa sun kashe mutane 15 a juma’ar da ta gabata. Kisan shine hari mafi girma da Lakurawa suka kai kawo yanzu.

Su wane Lakurawa?

Sojin Najeriya sun ce Lakurawa na da alaƙa da ƙungiyar IS kuma suna aiki a jihohin Kebbi da Sokoto, kuma sun sun fito ne daga ƙasashen Mali da jamhuriyar Nijar inda suka kutsa Najeriya.

Lokaci na farko da Lakurawa suka bayyana a Najeriya shine a shekarar 2018, a lokacin da suka fara taimakawa jama’a wurin yaƙar ƴan bindiga kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

To sai dai daga bisani alaƙa ta yi tsami tskanin Lakurawa da mutanen gari, bayan da jama’a suka zargesu da fara sace musu shanu da kuma ƙaƙaba musu dokoki.

Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta Najeriya Edward Buba ya ce a farko ba a yi tunanin Lakurawa suna da wata barazana ba.

Ya ce sun ƙara fantsama a Najeriya bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar a watan Ulin 2023, bayan dakatar da sintrin sojin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Nijar a yankunan.

Shin wace barazana Lakurawa ke da ita?

Dama Najeriya na tsaka da yaƙi da ƴan bindiga da matsalolin tsaro daban-daban, kamar ƙungiyar Boko Haram da kuma wasu ƴan ta’addda dake da alaƙa da ISWAP.

Wani masanin tsaro James Barnett ya ce wani sabon rikici ka iya ƙara damalmala lamurra a ƙasar kasancewar dakarun soji sun jima suna yaki da matsaloli daban-daban.

James ya ce kasancewar Lakurawa sun fara wa’azi tare da sanya dokoki masu tsauri kan jama’a to yana alamta cewar suna da wani babban ƙudiri na ƙara fantsama da kuma samun ƙarfin iko a Najeriya.

Wane mataki Najeriya ta ɗauka kan wannan barazana?

Dakarun sojin Najeriya sun dawo aikin haɗin gwiwa tare da sojin Nijar kuma sun yi alƙawarin yaƙar Lakurawa.

Ziyarar da mai riƙon muƙamin hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya kai jihar Sokoto domin ƙarawa dakarunsu kaimi ya nuna irin muhimmancin da sojin ƙasar suka bawa batun a yanzu.

Oluyede ya buƙaci gudunmawa da goyan bayan al’ummar dake rayuwa a yankunan da matsalolin tsaron ke faruwa domin yaƙar matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)