An sanar da rasuwar shahararren mawakin kasar Guinea Mory Kante yana da shekaru 70.
Dangane ga labaran da kafafen yada labaran cikin gidan suka rawaito, Kante wanda ya kasance ya na jinya a wani asibitin dake babban birnin kasar Conakry ya rasu.
Kante wanda aka haifa a ranar 29 ga watan Maris shekarar 1950 a garin Kissidougou ya kasance sananne a fadin duniya a shekarar 1977 da ya rera wakar "Ye ke ye ke"
Mory Kante, ya kasance mawakin Afirka da ya fi siyar da wakoki a kasuwar duniya.