Prime ministan ƙasar Ousmane Sonko ne ya bayyana hakan bayan shan alwashin daidaita tsarin fitar da man fetur na ƙasar da ya dauka.
Ƙasar ta yammacin Afrika ta shiga cikin jerin ƙasashe masu fitar da man fetur a watan Yulin da ya gabata kuma ta kammala duk wani shirye-shirye don fara fitar da iskar Gas a ƙarshen shekarar da muke ciki.
Tun bayan da aka rantsar da shi a watan Maris ɗin da ya gabata Shugaban ƙasar Bassirou Dimomaye Faye ya sha alwashin gudanar da bincike da kuma sanya idanu a fannin na man fetur da iskar Gas don hana duk wata almundahana shiga.
Sabuwar gwamnatin ta ce yarjejeniyoyin man fetur ɗin da tsohuwar gwamnati ta ƙulla da ƙasashe da kuma manyan kamfanonin duniya ba zai amfani ƙasar da komai ba.
A wajen taron ƙaddamar da kwamitin Sonko ya ce abin takaici ne yadda tsohuwar gwamnati ta shiga yarjejeniya bayan tana gani baro-baro cewa ka’idojin zasu cutar da ƙasar ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI