A dai ranar 1 ga watan Disambar shekarar 1944 ne sojojin Faransa suka buɗe wuta kan sojojin Senegal kusan dubu 1 da dari 600, da Jamus ta kama a lokacin da suke yiwa Faransa yaƙi, bayan da aka dawo dasu sansanin sojoji na Thiaroye, sakamakon takaddamar da ta shiga tsakani kan biyansu hakkokinsu.
A hukumance a lokacin, Faransa ta ce mutane 35 sojojinta suka kashe, duk da cewa masana tarihi sun ce adadin ya kai dari 4.
Tun daga lokacin ne kuma ake takaddama tsakanin ƙasashen biyu, inda Senegal ke buƙatar Faransa ta amince cewar kisan gilla ne ta aikatawa sojojinta, amma hakan bata samu ba sai a makon daya gabata, inda shugaba Emmanuel Macron ya tabbatar da hakan a cikin wani sakon da ya aike kan bikin na wannan rana.
A lokacin da shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ke gabatar da jawabi a wajen bikin, ya ce abin a yaba ne yadda Macro ya amince da kisan gillar da sojojinsu suka yi, don haka ya ce za a sanar da dalibai labarin kisan na Thiaroye.
Bikin ciki shekaru 80 da aikata kisan gillar dai ya samu halartar shugabannin ƙasashen Mauritania da Comoros da Gabon da Gambia da kuma Guinea-Bissau sai ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI