Sanarwar Shugaban na Senegal na zuwa yan lokuta bayan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amsa cewa sojojin Faransa na wancan lokaci ne suka aikata kisan kiyashi da aka yi wa sojojin Senegal a shekarar 1944.
Shugaban na Senegal ya yaba da amincewar amma ya ce ficewar dakarun Faransa daga Senegal,alheri ne ga kasar Senegal domin ci gaba da kasancewar su ya sabawa tsarin Senegal, domin a cewar sa “Senegal kasa ce mai cin gashin kanta,kuma diyaucin kasar bai amince da kasancewar sansanonin soji na wata kasa a kasar ba.
Shugaba Faye ya hau kan karagar mulki a zaben da aka yi a watan Maris 2024 inda ya yi alkawarin tabbatar da ikon Senegal da kuma kawo karshen dogaro ga kasashen ketare. Sai dai ya ci gaba da cewa wannan doka ba ta na nufin kawo karshen hulda da Faransa ba .
Shugaban na Senegal a karshe y ana mai cewa "a yau, kasar China ita ce babbar abokiyar cinikayyar Senegal ta fuskar zuba jari da cinikayya, kuma China ba ta da sojojinta a Senegal.
Wasu majiyoyin gwamnatin Faransa biyu sun shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP a wannan shekara cewa kasar na neman rage yawan sojojinta a nahiyar Afirka - daga dakaru 350 zuwa 100 a Senegal da Gabon da kuma 300 a Chadi daga 1,000 da 100 a Ivory Coast daga 600.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI