Saudi Arabia, OIC sun kira taron tallafawa Yankin Sahel, Tafkin Chadi

Saudi Arabia, OIC sun kira taron tallafawa Yankin Sahel, Tafkin Chadi

Taron wanda zai gudana a karkashin ministoci da kuma goyan bayan kungiyar kasashe Musulmi ta duniya ta IOC za’a gudanar da shi ne a ranar litinin mai zuwa, wato 26 ga watan Oktoba.

Majalisar dinkin duniya ta ce akalla mutane kusan miliyan 33 ke bukatar taimakon jinkai da kuma kariya a yankin, cikin su harda wasu miliyan 11 da suka rasa matsugunansu sakamakon rikice rikice a wadannan yankuna biyu.

Sanarwar hadin gwuiwar da aka gabatar dangane da gidauniyar ta nuna cewar Gidauniyar Sarki Salman bin Abdulaziz da kungiyar kasashe Musulmi ta OIC tare da Ofishin jinkai na Majalisar dinkin duniya da kuma Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ne za su jagoranci taron domin tara wadannan kudade domin ceto rayukan fararen hular da rikice rikice suka ritsa da su.

Wasu 'yan gudun hijira a Maiduguri, wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihar Borno. Wasu 'yan gudun hijira a Maiduguri, wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihar Borno. © REUTERS/Afolabi Sotunde

Sanarwar ta kara da cewar yankin Sahel da kuma Tafkin Chadi ya kwashe shekaru da dama yana fama da matsaloli daban daban, wadanda suka dakushe ci gaban sa ta fannin zaman lafiya da tattalin arziki da kuma jin dadin rayuwa.

Tsukewar Tafkin Chadi ya shafi miliyoyin jama’ar da suka dogara da shi domin rayuwa, tare da haifar da rikice rikicen da ake bukatar daukar matakan gaggawa domin samar da mafita a kai.

Dr Abdullahi Al Rabeeah, shugaban kula da kungiyar Jinkai ta Sarki Salman ya ce sun fahimci muhimmancin kai dauki ga jama’ar wadannan yankuna biyu na Sahel da Tafkin Chadi, saboda haka suka dauki wannan mataki mai matukar muhimmanci domin tara gudumawar da za’a taimakawa miliyoyin jama’a da zummar rage musu radadin matsalar da suke fuskanta.

Taron kasashen Larabawa Taron kasashen Larabawa REUTERS/Osman Orsal

Sakatare Janar na kungiyar kasashen Musulmi ta duniya, OIC, Hissein Brahim Taha ya bayyana farin cikinsa na aiwatar da yarjejeniyar da ministocin kasashen Musulmi suka amince wajen shirya wannan taro da zummar samar da taimakon da ake bukata da za’a kai dauki ga mutanen da matsalar ta shafa.

Joyce Msuya, mai rike da shugabancin hukumar jinkai ta Majalisar dinkin duniya ta bayyana Sahel da Tafkin Chadi a matsayin wadanda suke fuskantar dimbin matsalolin da ya dace a taimaka musu.

Shi kuwa shugaban kwamitin kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar, Filippo Grandi ya jinjinawa Saudi Arabia da OIC da kuma kawayen su ne saboda wannan yunkuri na ceto miliyoyin jama’ar da suka tagayyara sakamakon wadanan rikice rikice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)