Firaministan Libiya Fayiz Al-Sarraj ya yi kira ga kasashen duniya da suke goya baya ga dan tawaye Haftar Khalifa da su sauya tunani game da matakin da suka dauka.
Firaministan na Libiya ya yi jawabi ta hanyar sadarwar bidiyo a zama na biyu na Babban taron Majalisar Dinkin DUniya karo na 75.
Ya bukaci kasashen duniya da suke goya baya ga dan tawaye Haftar Khalifa da su sauya tunani game da matakin da suka dauka, kuma su yi aiki tare da Gwamnatin Sulhun Kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.
Sarraj ya kuma ce suna kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta gudanar da bincike game da take hakkokin dan adam da ake yi a garin Sirte.
Firaministan ya kuma kara da cewar ya zama wajibi a yi kwaskwarima ga aiyukan kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ba su dace da wannan lokacin ba.