Wannan na zuwa ne, yayin da aka shirya wani babban taron kasashen wannan yanki, domin tattaunawa tare da nemo mafita kan matsalolin da ke addabar yankin.
Taron wanda ke gudana a birnin Maiduguri da ke jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, rahotanni sun ce, zai mayar da hankali kan yadda za a bunkasa yankin, la'akari da yadda hare-haren masu tayar da kayar baya, musamman Boko Haram ya daidaita yankn.
Taron ya samu halartar manyan baki, musamman daga kasashen yankin. © RFIKasashen yankin Tafkin Chadi dai, sun jima suna fama da tashe-tashen hankula na masu dauke da makamai, abin da ya haifar da koma baya a fannoni da dama, musamman tsaro da tattalin arziki.
Rikicin yankin, ya tilastawa miliyoyin mutane tserewa daga matsugunansu domin neman mafaka, inda dubbai suka mutu, ciki kuwa har da mata da kananan yara.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton da bilyaminu Yusuf ya hada daga wurin taron.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI