
Rahotanni sun ce da dama daga cikinsu, daman su na gudun hijira ne a cikin kasar, inda a yanzu suka kara yin nisa daga yankunan da ke cikin barazana domin neman mafaka.
Galibin dai waɗanda su ke shiga Burundin, hukumomin ƙasar sun ce, mata ne da ƙananan yara da suke gujewa tashe-tashen hankulan da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a Gabashin Jamhuriyar Congo.
Yayin da faɗan ke ƙara kusanto wa garin Uvira, wato garin da ke kan iyakar Burundi da Congo, ana fargabar rikicin zai kara rincaɓewa.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta yaba wa matakin da Burundi ta ɗauka na bai wa ‘yan gudun hijirar mafaka, tare da tabbatar da cewa za ta basu taimakon gaggawa, musamman a ɓangaren da ya shafi taimakon jin kai.
Waɗannan sabbin bakin hauren dai ‘yan kasar Congo ne wadanda tuni aka raba su da muhallansu sakamakon tashe-tashen hankula da suka faru a baya, wanda yanzu haka aka tilasta musu yin gudun hijira saboda sabon faɗan da ya sake barkewa.
Wasu sun yi tattaki tun daga garin Goma, mai tazarar ɗarurruwan kilomita zuwa Arewaci, abin da ya kasance babbar damuwa ga mutanen da basu ji basu gani ba.
Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijirar ta ce, tana aiki tuƙuru don taimaka wa waɗannan 'yan gudun hijirar, musamman ma a bangaren abinci da ruwan sha da dai sauran abubuwan buƙatun yau da kullum.
Gwamnatin Burundi ta fitar da sanarwar cewa, tana shirin ware wasu filaye domin fadada matsuguni ga 'yan gudun hijirar, haɗi da samar musu da tallafin da suke buƙata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI