Sama da mutum dubu 100 ne suka tserewa rikicin Congo cikin mako guda - MDD

Sama da mutum dubu 100 ne suka tserewa rikicin Congo cikin mako guda - MDD

A ranar Asabar ne 'yan tawayen M23 suka karbe iko da Masisi, wani muhimmin gari a Jamhuriyar Congo mai arzikin ma'adinai.

"Tsakanin 1 zuwa 3 ga watan Janairun 2025, munanan arangama tsakanin sojojin Congo da wata kungiya mai dauke da makamai a Masisi dake lardin Kivu ta Arewa, kimanin mutane 102,000 suka rasa matsugunansu, kamar yadda rahotannin cikin gida suka nuna," in ji ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD.

Ma’aikatar harkokin wajen Rwanda ta ce a baya-bayan nan ne ‘yan tawayen M23 suka kwace ikon wasu yankuna  daga mayakan Hutu, wadanda ake dangantawa da kisan kare dangi ga ‘yan kabilar Tutsi na Rwanda a shekarar 1994.

Ministan harkokin wajen kasar Olivier Nduhungirehe ya bayyana a cikin sanarwa cewa, yankuna da dama da ke yankin Masisi ke hannun kungiyar da ake zargi da aikata kisan kare dangi.

Sanarwar ministan, ta kuma yi tir da sukar da suke fuskanta daga hukumomi na duniya, da kuma yadda suka gaza yin Allah-wadai da yadda ake ci gaba da keta mutuncin kasar Congo.

Masisi, mai yawan al’umma kusan 40,000, tazarar kilomita 80 ne tsakaninsa da birnin Goma, na Arewacin Kivu.

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa, MSF, tace tsakanin ranakun Juma’a zuwa Litinin, mutum 75 ne suka karbi kulawa a wasu cibiyoyin lafiya da ke yankin.

Kungiyar 'yan tawayen M23 da Jamhuriyar Congo da Majalisar Dinkin Duniya suka ce makwabciyar kasar wato Rwanda da sojojinta ne ke goya musu baya, sun kwace yankunan gabashin Congo tun daga shekara ta 2021, lamarin da ya raba dubban mutane da muhallansu, tare da haifar da illa ga ayyukan jin kai.

An soke zaman sulhun da Angola ke jagoranta tsakanin shugaban Jamhuriyar Congo, Felix Tshisekedi, da takwaransa na Rwanda  Paul Kagame, a tsakiyar Disamba, sakamakon rashin amincewa da yarjejeniyar zaman lafiyar da bangarorin biyu suka yi.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta dauki tsawon shekaru 30 tana fama da tashe-tashen hankula na masu dauke da makamai da suka fito daga ciki da kuma wajen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)