Sama da mutanne dubu 18 sun harbu da cutar ƙyandar biri a Afrika

Sama da mutanne dubu 18 sun harbu da cutar ƙyandar biri a Afrika

Wannan adadi sun harbu ne da ilahirin nau’uka 3 na wannan cuta, har da sabon nau’in Clade 1b, wand ay tilasta wa Hukumar Lafiya ta Duniya ayyana dokar ta baci a ranar Laraba da ta gabata.

 

Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutane dubu 3 da 101 sun kamu da cutar, a yayin da ake zaton dubu 15 da 636 su na da wannan cuta ta kyandar biri a ƙasashe 12 da  ke cikin ƙungiyar Tarayyar Afrika.

 

Mutane ɗari 5 da 41 ne suka mutu sakamakon harbuwa da wannan cuta kamar yadda  cibiyar yaƙi da cutuka ta  Afrika ta bayyana a wata sanarwa.

 

A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda nan ne cutar ta fi ƙamari, kuma aka fara samun nau’in Clade 1b na cutar a watan Satumban shekarar 2023, mahukunta sun sanar da samun mutane 1005 da suka harbu da cutar, da waɗanda suka mutu 24 a cikin mako guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)