Sakamakon hare-hare sama da 700 na ta'addanci da aka kai a shekarar da ta gabata a Yammacin Afirka, mutane dubu 2 da suka hada da sojoji ne suka rasa rayukansu.
Shugaban Kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) Jean-Claude Kassi Brou ya sanar da cewa, 'yan ta'adda na ci gaba da yin barazana a yankin.
Brou ya kara da cewa, har yanzu akwai matsalolin rashin tsaro da fargaba a kasashen ECOWAS.
Ya ce, "Duk da kokarin kasashe mambobin ECOWAS amma a shekarar 2020 an kai hare-haren ta'addanci sama da 700 tare da kashe a kalla mutane dubu 2 da suka hada da sojoji da fararen hula."
Brou ya shaida cewa, an samu mafi yawan hare-haren a kasashen Burkina Faso, Mali, Nijar da Najeriya, kuma adadin mutanen da aka raba da matsugunansu a yankunan ya karu sosai.
Shugaban na ECOWAS ya yi kira ga shugabannin yankin da su kara azama don ganin an kawo karshen matsalolin tsaron da ake fuskanta.