Kafafen yaɗa labaran Sudan sun ruwaito cewa mutane da dama sun bace sakamakon fashewar madatsar ruwan Arbaat, wadda ta kasance inda al’ummar jihar Port Sudan ke samun ruwan sha, klamarin da ya haddasa mummunar ambaliya.
Ambaliyar ta lalata gidaje tare da share ababen hawa, kana ta tilasta wa jama’a arcewa zuwa tudun mun tsira, kamar yadda wani ganau ya bayyana.
Ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a Sudana bazara sun riga sun shafi aƙalla mutane dubu 317 tare da kashe mutane 39, acewar ofishin hukumar agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.
Mazauna yankin sun ce a cikin daren Asabar ne madatsar ruwan ta fashe sakamakon ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da aka yi, kuma samun bayanai ya kasance da wahala duba da rashin kyaun layukan sadarwa.
Wannan lamari na barazanar ta’azzara cutar kwalara da ta bullla a ƙasar da ke fama da yakin da ya ɓarke tun a watan Afrilun shekarar 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI