Da dama daga cikin mutanen da aka kawo asibiti na bukatar karin sassan jini inda likitoci suka bayyana karancin kayan aiki wanda hakan ba zai ba su damar kulawa da wadanda suka jikkata.
A cewar sabon rahoto daga yankin , mutane 54 ne suka mutu sakamakon tashin bam din. A kudancin babban birnin kasar, "farar hula biyu ne suka mutu" sakamakon wani hari ta sama da aka kai kan wani yanki da dakarun sa kai ma FSR ke iko da shi, a cewar cibiyar sadarwa ta gida "Cell Intervention Cells".
Wani tankin yaki a wani yanki a kasar Sudan REUTERS - El Tayeb SiddigTun daga watan Afrilun 2023, dakarun sa kai na FSR ke ci gaba da yaki da sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhane, rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da raba sama da miliyan 12 da gidajensu.
Wani da ya tsira daga harin ya shaidawa AFP cewa, rokokin sun fado ne a tsakiyar kasuwar kayan lambu, shi ya sa ake samun asarar rayuka da jikkata da dama.
Mutanen da suka shaida harin na yau Asabar, wanda shi ne na baya-bayan nan da aka kai wa wata kasuwa, sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, makaman atilare da jirage marasa matuka, sun fito ne daga yammacin Omdurman, yankin da har yanzu dakarun sa kai na FSR ke iko da shi.
Wani mazaunin wani yanki da ke kudu da Omdurman ya ce, "Roka da manyan bindigogi suna fadowa," ya kuma karasa da cewa dakarun na RSF sun kaddamar da hari a lokaci guda kan tituna da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI