Wata ƙungiyar lauyoyi da ke bibiyar yadda rikicin ke gudana, ta ce RSF ta kai hari sassa daban-daban na birnin da manyan bindigun atilari, daga cikin wuraren kuwa har da babbar kasuwan yankin.
Haka nan kungiyar ta ce sojojin ƙasar ta Sudan sun kashe akalla mutane 4 a al-Souki da ke kusa na Sennar a ya yin harin, sannan RSF ta sake kashe mutun daya a el-Obeid tare da raunata wasu 17, a wani hari na daban data kai a kokarin kwace ikon yankin da take yi.
Jagoran sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan. © AFPRundunar RSF wacce tuni ta kwace ikon mafi yawancin sassan birnin Sennar, itace ke kula da ikon kusan rabin ƙasar ta Sudan musamman yankin kudu maso gabashin sa.
Yakin ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da na RSF da aka kwashe sama da watanni 18 anayi, ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane da raba wasu miliyoyi da muhallansu tare kuma da haifar da barkewar yunwa mafi muni a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI