Sama da manyan motoci 700 ɗauke da kayan agaji na dab da isa Sudan

Sama da manyan motoci 700 ɗauke da kayan agaji na dab da isa Sudan

Bayanan hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce motocin na ɗauke da tan dubu 17,500 na abinci, wanda zai isa a ciyar da mutane akalla miliyan 1 da rabi.

Mai magana da yawun hukumar Leni Kinzil ta shaidawa manema labarai a birnin Geneva cewa, tuni gwamnatin Sudan ta bada damar shigar da motoci 700 zuwa ƙasar kuma kowa ne lokaci lokaci daga yanzu za su fara shiga cikin ƙasar.

Leni ta ce wucewar da damuna ta yi, ya ƙara ta’azzara yunwar da jama’a ke ciki, don haka ya zama wajibi mahukunta su dubi al’ummar ƙasar da idon rahama.

Jami’ar ta ce babban fatan hukumar WFP a yanzu shi ne gwamnatin ƙasar ta ci gaba da bayar da haɗin kai a ƙoƙarin da ake yi na ganin anwadata mutanen da yaƙi ya daidaita da abinci.

Bayanai sun ce yankunan da za su fi amfana da abincin sun haɗar da Zamzam da kuma Darfur, inda a yanzu rikici tsakanin sojojin gwamnati da na RSF ya fi kamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)