Salva Kiir ya yi wata ganawar gaggawa da manyan jami'an tsaron Sudan ta Kudu

Salva Kiir ya yi wata ganawar gaggawa da manyan jami'an tsaron Sudan ta Kudu

A yammacin ranar Alhamis a gundumar Thongpiny, aka fuskanci musayar wuta a gidan tsohon shugaban hukumar liken asirin ,wani dan jarida na AFP ya lura da dimbin sojoji da safiyar Juma'a a kusa da gidan tsohon jami'in leken asirin, wanda ke tsare a gida tun watan Oktoba.

Bayan taron, kakakin rundunar sojojin Sudan ta Kudu (PDF), Lul Ruai Koang, ya tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne bayan da aka samu rashin fahimta tsakanin jami'an tsaron da aka tura domin bayar da kariya, da masu kare tsohon Shugaban.

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu AP - Gregorio Borgia

Koor da magajinsa sun halarci taron gaggawa, in ji ofishin Salva Kiir. Wani babban jami'in tsaro ya shaidawa jaridar Daily Sudans Post cewa taron ya taimaka wajen magance tashe-tashen hankula. "An samu kwanciyar hankali a Juba, kuma an ba Janar Akol da iyalansa tabbacin tsaron lafiyarsu," in ji shi.

Yanzu Koang da Koor sun amince su ƙaura "tare da ƙaunatacciyar matarsa, mai gadi da mai dafa abinci" a wani wuri a cikin birnin.

Koang ya fayyace cewa ba a tsare tsohon shugaban hukumar leken asirin ba. A cewarsa, an kashe mutane hudu, fararen hula biyu da sojoji biyu a yayin harbin.

Kanal John Kassara, kakakin 'yan sanda, ya yi kira ga gidan rediyon tawagar wanzar da zaman lafiya da tsaro a Sudan ta Kudu na Majalisar Dinkin Duniya (Minuss) da su sanya ido kan mazauna kusa da gidan Akol Koor.

Tun da farko Lul Ruai Koang ya shaidawa AFP cewa Akol Koor "yana nan a gida", ya kuma yi watsi da zargin da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta na cewa  Koor ya gudu zuwa harabar Majalisar Dinkin Duniya da ke Juba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)