Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu tare Ministar Harkokin Waje da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Saliyo Nabeela F. Tunis sun jagoranci bukin bude ofishin jakadancin Saliyo a Ankara Babban Birnin Turkiyya.
Minista Cavusoglu ya yi bayani a wajen bude ofishin da cewa, sun gamsu da yadda Saliyo ta bude ofishin jakadanci a Ankara wanda hakan zai kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen 2.
Cavusoglu ya ce akwai kamfanunnukan Turkiyya da dama da ke son zuwa Saliyo don zuba jaria Saliyo.
Ya ce "Akwai jarin kasuwanci na kusan dala miliyan 50 tsakanin Turkiyya da Saliyo wanda hakan wata alama ce mai kyau matuka. Ofishin jakadancin da aka bude zai kara habaka wannan jari."
A nata bangaren, Minista Tunis ta bayyana farin cikinta kan yadda a karon farko kasarta Saliyo ta bude ofishin jakadanci a Ankara wanda hakan wani sabon shafi ne da kasashen 2 suka shiga.
Tunis ta kuma shaida cewar abun gamsuwa ne yadda Turkiyya ke kara samun karfi da karbuwa a Afirka, kuma ana samun ci gaba a dangantakar siyasa, tattalin arziki da girmama juna tsakanin Turkiyya da kasashen yankin.
Ministar ta kuma ce, kamfanunnukan Turkiyya da dama sun zuba jari a Saliyo a bangarorin makamashi, aiyukan noma da gine-gine.
Ta ce "Misali shi ne Freetown, wanda kamfanin Turkiyya ne ke samar da kaso 50 cikin 100 na makamashin da ke bukata a garin. Akwai wani kamfanin Turkiyya da ke gudanar da aikin fadada filin tashi da saukar jiragen sama a kasarmu."