Sabuwar nau’in Korona, Najeriya ta kaddamar da sabbin tsaruka

Sabuwar nau’in Korona, Najeriya ta kaddamar da sabbin tsaruka

Kasar Najeriya ta bayyana daukar wasu sabbin matakai akan fasinjojin dake fitowa daga kasashen Birtaniya da Afirka ta Kudu kasancewar samun sabuwar cutar Korona da aka yi a kasashen.

Shugaban dake kula da matakan dakile cutar korona a Najeriya Sani Aliyu ya bayyana cewa kasar zata fara daukar sabbin matakai akan sabuwar kwayar cutar ta Korona.

Akan haka Aliyu ya bayyana cewa daga ranar 28 ga watan Disamba dukannin fasinjojin da zasu shigo kasar kai tsaye daga Birtaniya ko Afirka ta Kudu zasu gudanar da gwajin kwayar cutar Korona.

Fasinjojin zasu yi rajista ne a kafar yanar gizon “Nigerian international travel portal” inda zasu cike tambayoyi da kuma sanya takardan shaidar gwajin kwayar cutar COVID-19 PCR wanda bai wuce kwanaki biyar da yinsa ba.


News Source:   ()