A karon farko a hukumance an mika sabon ginin da aka samarwa sabuwar gwamnatin Libiya ga jami'anta.
Kakakin Firaminista Abdulhamid Al-Dibabi, Muhammad Hammude ya shaida cewa, an mikawa gwamnatin ginin Majalisar Ministoci a hukumance.
Hammude ya ce, "Wannan ne gini na farko da aka mikawa Dibaybi a hukumance a kasar.
Sanarwar da Sashen Yada Labarai na Fadar Firaministan ya fitar ta ce, Dibaybi ya gudanar da taro na farko a ofishin tare da daraktoci da masu aikin gwamnati.
An tattauna kan yadda za a samar da tsarin sadarwa da aiyukan hadin kai tsakanin hukumomin gwamnatin Libiya daban-daban.
A ranar 10 ga Maris bayan taron Majalisar Ministoci na kwanaki 3 a garin Sirte na Libiya, an jefa kuri'ar amincewa da gwamnatin Dibaybi.