Sabuwar gwamnatin Libiya ta fara a aiki

Sabuwar gwamnatin Libiya ta fara a aiki

A Libiya, Muhammad Al-Manfi ya karbi ragamar jagoranci daga hannun Faiz Al-Sarraj.

A yayin bukin mika mulkin da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Tarabulus, Firaminista Abdulhamid Dibaybi ya samu damar halarta.

A jawabin da Manfi ya yi ya ce, "Yau muna ganin wata sabuwar hanya ta wanzar da zaman lafiya."

Ya ce, nan da karshen shekara za a baiwa 'yan kasar Libiya damar zabe 'Yan majalisar da za su wakilce su.

Sarraj kuma ya taya murna ga sabuwar gwamnati da aka jefawa kuri'ar amincewa.

Sarraj ya bayyana cewa, "Mika mulkin a wannan rana na wakiltar samar da gwamnati cikin lumana."

A ranar 10 ga Maris bayan taron Majalisar Ministoci na kwanaki 3 a garin Sirte na Libiya, an jefa kuri'ar amincewa da gwamnatin Dibaybi.


News Source:   ()