An bayyana bulluwar cutar Ebola a karon farko tun daga ranar 4 ga watan Maris a kasar Guinea.
A shafin Twitter Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ce aka bayyana cewa an samu mutum daya dauke da kwayar cutar Ebola a yankin Soulouta dake Kudu maso gabashin kasar Guinea a Nahiyar Afirka.
An bayyana cewa daga ranar 4 ga watan Maris kawo yanzu ba a samu cutar Ebola a kasar Guinea ba.
Amma a halin yanzu abin bakin ciki ne yadda aka samu wani da cutar Ebola a kasar.
Tuni dai an fara daukar muhimman matakai hana yaduwar cutar a yankin.
A ranar 13 ga watan Febrairu aka bayyana bulluwar sabuwar cutar Ebola a kasar Guinea.