Garin dai na daga cikin kauyuka da dama da aka kai wa hari a gabashin jihar El Gezira tun bayan sauya sheka da babban kwamandan RSF ya yi, lamarin da ya haifar da kai hare-haren ramuwar gayya da ya raba mutane sama da 135,000 da muhallansu.
Yakin da ake gwabzawa tsakanin dakarun biyu ya haifar da matsalar jin kai mafi girma a duniya, inda sama da mutane miliyan 11 suka rasa matsugunansu tare da jefa wasu da dama cikin tsananin yunwa inda wasu kuma har yanzu ke ci gaba da tserewa zuwa kasashen ketare.
Kungiyar Likitocin kasar ta ce ayyukan ta’asarar da dakarun RSF ke aiwatarwa ya haifar da tarnaki ga bangaren kiwon lafiya, inda a yanzu ake samun tururwar wadanda suke fama da kwalara a asibitoci.
Wannan sabuwar cuta sanarwar kungiyar ta ce na da nasaba ne da rashin samun cikakkun bayanai kan musabbabin bullarta.
Wani mutum da ya zanta da kamfanin dillancin labaran reuters ya ce wasu ‘yan uwansa uku sun mutu sakamakon rashin lafiya.
Wadanda ke son ficewa dole ne su biya makudan kudade a wuraren bincike na RSF.
A cewar masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya, an fara kawanya ne a ranar 29 ga watan Oktoba lokacin da RSF ta kai hari garin, inda ta kashe mutane biyar.
Hilaliya dai gida ce ga iyalan kwamanda Abuagla Keikal da ya sauya sheka, wanda mazauna yankin suka ce sama da mutum 50,000 ke rayuwa a kauyen ciki kuwa har da mutanen da suke tserewa rikii a yankunansu.
Hotunan tauraron dan adam daga wani rahoton dakin binciken agaji na Yale ya nuna yadda aka samu karuwar kaburbura a makabartu, musamman a kauyukan da ke Gezira, tun bayan da aka fara kai hare-haren ramuwar gayya a karshen watan Oktoba.
Har ila yau, an kuma gano yadda aka kona filayen noma a kauyen Azzrag, Wanda ake zargin mayakan na RSF ne suka aiwatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI