Sabon shugaban Kasar Zambiya da ya lashe zabe a ranar 12 ga Agusta Hakainde Hichilema ya karbi rantsuwar kama aiki.
Bayan karbar rantsuwa, an mikawa Hichilema mulkin Zambiya.
Sabon Shugaban na Zambiya mai shekaru 59 ya karbi rntsuwar kama aiki a filin wasanni na kasa da ke Lusaka Babban Birnin Kasar.
Hichilema ya rantse da bible a gaban dubunnan mutanen da suka halarci bukin rantsuwar.
Hichilema zai jagoranci Zambiya har nan da 2026. Sabon Shugaban na daya daga cikin attajiran kasar.