Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya ta EFCC Abdulrasheed Bawa ya ja kunnen ma'aikatar hukumar da rashin zuwa wajen aiki da wuri inda ya tabbatar da cewa duk wanda yazo makare ba zai samu cikekken albashi ba.
Kafafen yada labaran cikin gidan Najeriya sun rawaito irin jan kunnen da sabon shugaban hukumar EFCC ta Najeriya ya yiwa daukacin ma'aikatar hukumar akan rashin zuwa aiki da wuri da kuma tashi gabanin lokaci ya cika.
Bawa, ya bayyana cewa ya zama wajibi ga dukkanin ma'aikatan hukumar dama na sauran ma'aikatu da su tabbatar da sun kasance a wurin aiki da karfe 8 na safe su kuma tashi da karfe 5 na marece.
Ya yi barazanar cewa duk wanda ya zabi zuwa wajen aiki da karfe 9 ya kuma tashi da karfe 3 kar ya yi tunanin zai karbe cikekken albashinsa.
Da yawan al'umma Najeriya na kallon wannan matakin na sabon shugaban hukumar ta EFCC a Najeriya a matsayin "aiki daga gida yake farawa"