Sabon rikici ya ɓarke a Khartoum tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF

Sabon rikici ya ɓarke a Khartoum tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF

Bayanai sun ce sabon faɗan ya ɓarke ne da sanyin safiyar yau Alhamis bayan da sojojin na Sudan suka ƙaddamar da farmaki, wanda shi ne irinsa na farko cikin watanni da zummar sake ƙwato yankunan babban birnin kasar da ke karkashin ikon dakarun na RSF da suka yi tawaye.

Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce a halin yanzu sojijin Sudan sun samu nasarar tsallaka wasu gadoji uku da suke da matuƙar muhimmanci da ke kan kogin Nilu, wanda ya raba sashin birnin na Khartoum da ke ƙarƙashin ikon gwamnati da kuma wanda mayakan RSF ke riƙe da su.

Makwanni  bayan ɓarkewar ƙazamin faɗan Sudan ne dai rahotanni suka bayyana yadda mayakan RSF masu biyayya ga Muhd Hamdan Daglo, suka kwace yankuna da dama da ke birnin Khartoum bayan fatattakar dakaru masu biyayya ga shugaba Abdel Fattah al-Burhan.

Zuwa yanzu, rayukan dubban mutane sun salwanta a yaƙin na Sudan, adadin da har yanzu ba a tantance ba, kodayake akwai masu kiyasin yawan mamatan na tsakanin mutane dubu 20 ne zuwa dubu 150.

Baya ga hasarar rayukan da aka samu, mutane fiye da miliyan 10 suka rasa muhalllansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)