Wani sauro mai sanya zazzabi da ba a taba ganin irin sa a Afirka ba ya bulla a Itopiya wanda hakan ya janyo firgici a tsakanin jama'ar kasar.
Sakamakon binciken da Sashen Likitanci na Jami'ar Radbound ta Holan da Cibiyar Bincike ta Hansen da ke Itopiya suka gudanar ya bayyana cewa, wannan sabon nau'in sauro da ya bulla a Afirka na sanya fargaba game da zazzabin da ya ke janyowa.
Dr. Fitsum Tadesse na Jami'ar Itopiya da ke Addis Ababa ya bayyana cewar, sauron na farwa abubuwa masu rai, kuma idan aka dauki matakan da suka kamata a kan lokaci to za a iya hana shi yaduwa, amma idn ka yi rashin nasarar hakan to za a fuskanci hatsarin zazzabi a yankunan Afirka da dama.
Akwai nau'ikan sauro 60 da ke sakawa mutane zazzabi kuma a kowacce shekara zazzabin cizon sauro na yin ajalin mutane dubu 400,000 a duniya.