Rundunar sojin Congo ta tabbatar da nasarar ƴan tawayen M23 a gabashin ƙasar

Rundunar sojin Congo ta tabbatar da nasarar ƴan tawayen M23 a gabashin ƙasar

Kakakin rundunar sojin ƙasar, Janar Sylvain Ekenge ne ya tabbatar da haka a  wata sanarwa ta ba sa bambam daga soji, inda ya ce ‘abokan gaba’ sun yi nasara a garuruwan Bwereman da Minova.

Shigar garin Minova hannun ƴan tawayen M23, waɗanda ake zargin sojin Rwanda da mara wa baya, ya sake jefa babban birnin yankin, wato Goma cikin yanayi na ƙawanya, a yaƙin da tuni ya ɗaiɗaita ɗaruruwan dubbai.

Wata majiyar soji ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa tun da farko cewa, ana ci gaba da musayar wuta, amma kuma ya ce lallai ƴan tawaye sun karɓe wannan gari mai mahimmanci.

Tun bayan da ƙungiyar ƴan tawayen M23 ta sake dawowa a shekarar 2021, ta ci gaba da yin tasiri a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Amma karɓe iko da garin Minova, shi ne tasiri na baya-bayan nan da ta yi a cikin ƴan makwannin nan.

Garin Minova, alkarya ce mai mazauna da yawansu ya kai dubu 65 wadda lardin Kudancin Kivu ne, kuma yana zaune ne a tsakanin tafkin Kivu da tsaunukan Masisi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)