Sashin bincike na musamman da ke kula da laifuffukan yaki da cin zarafin bil’adama na rundunar ƴan sandan Norway Kripos ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce sun kama wani da ake zargi, duk da cewa ba su bayyana sunansa ba.
Rundunar ta ce tana zargin mutumin da ta kaman, na taka muhimmiyar rawa a rikicin ƴan aware da ake samu a Cameroon.
Sai dai tun da farko, wata majiya ta tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa mutumin da rununar ta kama ba kowa bane face Ayaba.
Wannan ne dai karo na farko da rundunar ƴan sandan Norway ta taɓa kama wani da ake zargi da aikata laifukan tunzura jama'a da kuma cin zarafin bil’adama.
Tun a shekarar 2016 ne dai Cameroon ke fama da rikici a yankunan arewa maso yamma da kuma kudu maso yammacin ƙasar da ke amfani da Turancin Ingilishi, tsakanin ƴan aware da dakarun gwamnati.
Rikicin dai ya samo asali ne bayan da shugaba Paul Biya ya murkushe wata zanga-zangar lumana da ake yi a yankunan.
A cewar wata ƙungiya da ke kula riki ta ƙasa da ƙasa, sama da mutane dubu 6 ne dai suka rasa rayukansu a rikicin, sannan aka raba wasu kimanin miliyan daya da gidajensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI