Runduna sojin Mali ta hallaka manyan 'yan tawayen Abzinawa a Tinzaouatene

Runduna sojin Mali ta hallaka manyan 'yan tawayen Abzinawa a Tinzaouatene

Wannan dai shine karo na farko da ƴan tawayen suka rasa jagorori da dama a lokaci guda, tun bayan da suka fara ta da ƙayar baya a shekarar 2012 a yayin wani farmaki da aka kai musu.

A wata sanarwa da kakakin ƴan tawayen Mohamed Elmaouloud Ramadane ya fitar, ta ce hare-haren jiragen saman marasa matuka sun kashe jagororin nasu ne a ranar 1 ga Disamban nan a garin Tinzaouatine, kusa da iyakar ƙasar da Aljeriya.

A yammacin lahadin da ta gabata ne babban hafsan sojin kasar ta Mali ya tabbatar da mutuwar shugabannin 'yan tawayen, a wata sanarwa da ya fitar a gidan talabijin ɗin ƙasar, wadda ta bayyana a matsayin 'yan ta'adda a ƙasar ta Mali.

A yayin da kakakin sojin ƙasar ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar koma bayaga ƴan tawayen wanda cike gurbin zayyi matuƙar wahala a garesu, sai dai wannan koma bayan da suka samu ba yana nufin an kawo karshen yakin a cewar Elmaouloud.

Ya kuma ci gaba da cewa Gwamnatin sojin kasar ta nuna wadannan hare-hare ta sama na nuni da ba ta tsoron yin amfani da kadarorin jiragen da ta samu a duk lokacin da ya kamata.

A wannan mako ne dai ƴan tawaye na bangarori daban daban ke haduwa a wanna wuri domin haɗa ƙaƙƙarfar tawagar guda ta mayaka da zasu fafata  da dakarun gwamnatin ƙasar ta  Mali, amma dakarun sojin ƙasar suka yi nasarar  dirar mikiya akansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)