Ƴansanda 200 ne yanzu haka suka haɗe da ƴan uwansu 600 da tun tuni suke a ƙasar don yaƙar ƴandaban, duk kuwa da yadda Amurka ta sanar da katse tallafin da take bayarwa wajen yaƙi da ƴandaba a cikin ƙasar.
Baya ga ƴansandan na Kenya akwai kuma ƴansandan ƙasashen Jamaica da Guatemala da kuma El Salvador waɗanda ke taimaka wajen kawo ƙarshen tasirin ƴandaban dake ƙoƙarin kifar da gwamnatin ta Haiti.
Ƴansandan na Kenya 200 sun isa Haiti ne a dai dai lokacin da shugaba Donald Trump na Amurka ya kawo karshen tallafin dala miliyan 13 da rabi wanda Washington ke baiwa ƙasar ta Haiti.
A cewar shugaban aikin wanzar da zaman lafiyar a Haiti Godfrey Otunge tallafin na Amurka na matsayin kashi 3 cikin 100 da Haiti ke samu daga manyan ƙasashe a wani ɓangare na taimakon da take karɓa don yaƙi da matsalar ta ƴandaban da suka addabeta.
Sai dai Amurkan ta amince da tallafin dala miliyan 40 daya ƙunshi samar da motoci masu silke da sauran kayayyakin yaƙi ga Haiti.
Zuwa yanzu ƴandaban ne ke riƙe da kashi 85 na babban birnin Haiti wato Port-au-Prince kuma aikin wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Ɗinkin Duniyar na fuskantar ƙarancin kuɗin tafiyarwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI