
Bayanai sun ce galibin ƙungiyoyin da suka mara baya ga RSF a wannan tafiya dama can nada takun-saƙa tsakaninsu da gwamnatin Abdel Fattah al Burhan.
Tsawon watanni 20 kenan ana gwabza yaƙi tsakanin Sojin gwamnatin Sudan da takwarorinsu na dakarun kai ɗaukin gaggawa wato RSF inda ake tuhumar dukkanin ɓangarorin biyu da aikata laifukan yaƙi da ya kai ga kisan tarin fararen hula baya ga aikata fyaɗe da kuma azabtarwa.
Yanzu haka kaso mai yawa na sassan Sudan na hannun mayaƙan na RSF wanda bayanai ke cewa suna samun goyon bayan wasu ƙasashe ciki har da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ke taimaka musu da tarin makamai.
Tsawon lokaci ana ƙoƙarin hawa teburin sulhu tsakanin ɓangarorin biyu amma kowannensu ya na kawo cikas kodayake a baya-bayan nan al-Burhan da kansa yaƙi amincewa da zaman sulhun.
Fiye da mutum miliyan 7 wannan yaƙin ya tilastawa gudun hijira a Sudan inda Majalisar ɗinkin duniya ke cewa akwai buƙatar dala biliyan 8 don agazawa mutanen da suka tagayyara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI