A cikin wata sanarwa da jami’ar kula da ayyukan jin kai, ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Sudan Clementine Nkweta-Salami ta fitar, ta ce wasu dokoki da RSF ta sanya a yankin na Darfur, na haifar da tarnaƙi wajen gudanar da ayyukan ceton rayukan jama’a.
Dakarun na RSF da ke fafata yaƙi da sojojin Sudan tun a watan Afrelun shekarar 2023, sun kasance masu rike da ikon yankin na Darfur, musammann yadda su ka mamaye birnin El-Fasher da ke Arewacinsa a watan Mayun shekarar da ta gabata.
An dai ayyana ɓarkewar yunwa a wasu yankuna biyar na Arewacin Darfur, kuma ana zaton ta ƙara bazuwa zuwa wasu yankuna biyar nan da watan Mayu mai zuwa.
A cewar wasu alkaluma da wata ƙungiya da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, sun nuna cewa kimanin mutum miliyan 7 ne ke fuskantar yunwa a yankin na Darfur.
Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta buƙaci RSF ta sauƙaƙa dokokin da ta sanya a yankin, don bada damar isar da kayan agaji ga al’ummar da ke cikin tsananin buƙata.
Shi dai yaƙin na Sudan ya lakume rayukan ɗaruruwan mutane, ya kuma raba sama da mutum miliyan 12 da muhallansu, sannan akwai wasu kimanin miliyan 25 da ke fuskantar barazanar yunwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI