Tun a watan Janairu shekarar nan ne dai yankin ya kasance cikin shirin ko ta kwana a lokacin da kasar Habasha ta sanar da cewa za ta yi hayar wani yanki na gabar teku daga Somaliland, yankin da ya balle daga Somalia, domin gina sansanin sojin ruwa da tashar jiragen ruwa da zai mayar da hankali a bangaren kasuwanci.
Kasar Habasha da ba ta da tudu ta dade tana neman hanyar shiga teku, amma matakin ya harzuka kasar Somalia da ta ki amincewa da ’yancin cin gashin kan Somaliland da ta fara shelanta a shekarar 1991.
Mayakan Al Shebab © Farah Abdi Warsameh/APSomalia ta mayar da martani ne ta hanyar samun kusanci da babbar abokiyar hamayyar yankin Habasha wato Masar. Kasar Masar dai na da nata korafin da Habasha, musamman babbar madatsar ruwa ta Grand Renaissance da take ginawa a kan kogin Nilu wanda Alkahira ke ganin yana barazana ga samar da ruwan sha.
A ranar 14 ga watan Agusta, shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamoud ya ba da sanarwar yarjejeniyar soja ta "tarihi" da Masar.Omar Mahmood na kungiyar International Crisis Group ya ce " Somalia, kasar da tuni ta samu yawan makamai, a halin yanzu ana fuskantar yawaitar makamai da ake shigowa da su ba bisa ka’ida ba.
Rundunar Habasha © AFPMa'aikatar harkokin wajen kasar Habasha a ranar litinin ta na mai cewa ta damu musamman ganin cewa makamai da ake shigowa da su zasu je a hannun mayakan Al-Shabaab.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI