Rikicin siyasa da guguwar Chido sun maida tattalin arzikin Mozambique baya - IMF

Rikicin siyasa da guguwar Chido sun maida tattalin arzikin Mozambique baya - IMF

A zantawar da Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya yi da jami’in, ya ce a zango na biyu na wannan shekarar tattalin arzikin Mozambique ya ƙaru da shi 4.5, sai dai ya rikito a zango na uku zuwa kashi 3.7, kafin rikicin siyasar da ya dabaibaye ƙasar bayan zaɓen da aka gudanar.

Ya ce a duk lokacin da ƙasa ta fuskanci rikici ko afkuwar bala’oi tattalin arzikinta na durkushewa, kamar yadda suke hasashen zai faru da ƙasar a zango na hudu na wannan shekarar.

Harrison ya ce da zarar an warware rikicin siyasar ƙasar, za a ci gaba da tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnati da asusun kan lamunin shekaru uku da ta ke nema.

Tun bayan sanar da Daniel Chapo na jam’iyar Frelimo mai mulkin Mozambique a matsayin wanda ya lashen zaɓen ƙasar da aka gudanar, ƴan adawa suka fara gudanar da zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaɓen, bisa zargin tafka maguɗin da suka ce anyi.

A ranar 23 ga wannan watan ne kuma ake saran kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci kan wannan dambarwa, duk da cewa ƙungiyoyin fafaren hula da masu sharhi na ganin idan har aka tabbatar da nasarar jam’iyar Frelimo, al’amura ƙara taɓarɓarewa za su yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)