Rikicin M23: Ɗaruruwan mutane ne aka gudanar da jana'izarsu a Congo

Rikicin M23: Ɗaruruwan mutane ne aka gudanar da jana'izarsu a Congo

Kungiyar agajin gaggawa ta ƙasa da ƙasa Red Cross da sauran ƙungiyoyin ayyukan jinƙai ne suka gudanar da jana’izar, kamar dai yadda Myriam Favier shugabar ofishin Red Cross a Arewacin Kivu ta bayyana.

Myriam ta ce sun fuskanci ƙalubale da dama musamman ta fannin ƙarancin dakarun ajiye gawarwaki, kuma hakan ya faru ne saboda yadda rikicin ya haifar da katsewar wutar lantarki.

Hakazalika ta ce sun fuskanci matsalar ƙarancin filayen da ya kamata su yi amfani da su domin binne gawarwaki, yayin da a ɗaya bangare suka fuskanci matsalar tantance gawarwaki kafin binne su.

Ko a ranar Litin hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa daga ranar 26 ga watan janairu, aƙalla mutane 2,880 ne suka jikkata inda asibitoci suka cika maƙil a Goma.

Bayan kwace iko da birnin ne kuma mayaƙan M23 suka nufi Bukavu, yayin da suke shirin kutsawa babban birnin ƙasar Kinsasha, duk da cewa sun musanta hakan, sai dai a jiya M23 suka sanar da tsaigaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)